Cibiyar tattalin arziki ta Nijeriya ta yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar zai iya karuwa da kashi 5.5 a ma'aunin GDP idan aka dore da sauye-sauyen tattalin arzikin da ake yi.
Wannan na kunshe a cikin wani kundin hasashe na shekara ta 2025 da cibiyar ta kaddamar.
Shugaban Cibiyar Dr. Olusegun Omisakin, ya ce sun yi amannar idan aka ci gaba da fito wa da tsare-tsaren tattalin arziki Nijeriya za ta samu ci gaba.
Category
Labarai