Tankar mai ta sake fashewa a wani gidan mai a Jigawa
Wata tankar man fetur ta fashe a gidan mai na Shakkato da ke kan titin Kiyawa a Unguwar Takur Adua a cikin birnin Dutse a jihar Jigawa.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar dakon man fetur ke sauke man a ranar Alhamis da daddare.
Sai dai rahotanni sun ce ma’aikatan kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar da wuri.