Sufetan 'yan sandan Nijeriya ya bada umurnin kamo maharan da suka kashe 'yan sanda a Borno


Sufetan 'yan sandan NIjeriya Kayode Egbetokun ya bayar da umurnin kamo maharan da suka kai hari a ofishin yanki na hedikwatar rundunar dake jihar Borno.

Harin da aka kai a ranar Talata ya yi sanadin mutuwar jami'ai biyu tare da jikkata wani jami'i daya, a lokacin wani musayar wuta da suka yi da maharan wadanda aka ci karfinsu tare da taimakon 'yan JTF.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ACP Olumiyiwa Adejobi, ya ce Sufetan 'yan sanda ya yi Allah wadai da harin kuma ya bayar da umurnin kamo maharan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp