Dakarun sojin Nijeriya sun tarwatsa maboyar kasurgumin dan bindiga Bello Turji tare da lalata rumbun ajiyar abincinsa da kuma hallaka dansa daya.
Mai bin diddigi da lura da al'amurran tsaro a yankin Tabkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na X, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Makama yace rundunar hadaka ta Operation Fansan Yamma ce ta kai farmakin ta sama da kasa a maboyar Turji dake Fakai, cikin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Xamfara State.
Category
Labarai