Sojojin kasar Gabon sun sanya ranar zaben shugaban kasa, bayan hambarar da gwamnatin farar hula da Ali Bongo
Za a dai gudanar da zaben ne a ranar 12 ga watan Afrilun, 2025, wanda shugaban rikon kwarya bayan juyin mulkin Janar Brice Oligui Nguema, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.
A watan Agustan 2023 ne dai sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Ali Bongo da ya yi shekaru 14 yana shugabancin kasar, bayan da shi kuma ya karbi tafiyar da ragamar kasar bayan mahaifinsa Omar Bongo ya rasu wanda ya yi shekaru 41 yana mulkin kasar ta Gabon.