Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya sanar da cewa sojojin kasar Faransa za su fara ficewa daga kasar nan ba da jimawa ba.
A cikin wani jawabin sabuwar shekara da ya yi a gidan talabijin na kasar, Ouattara ya ce sojojin Faransa 600 da ke cikin kasar za su fara barin kasar a watan Janairun da muke ciki.
Ya kara da cewa za a hannunta mazaunin sojojin ga rundunar sojin kasar Côte d'Ivoire tare da kara zamanantar da aikinsu.