Rundunar sojin Najeriya ta ce nan ba dadewa ba ƙasurgumin dan ta'adda Bello Turji zai zo hannu.
Jami'in yada labaran rundunar ta operation Fansar Yamma Laftanal Kanal Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da makaman da rundunar ta ƙwace daga 'yan bindiga a karamar hukumar Kaura -Namoda dake jihar Zamfara.
Abubakar ya ce Turji na cigaba da wasan buya tsakaninsa da rundunar, sai dai ya tabbatar wa da 'yan Nijeriya rundunar za ta kamo shi.
Jami'in ya yaba tare da godewa al'umma bisa hadin kai da bayanan sirri da suke bai wa rundunar.
Category
Labarai