Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Lahadi zuwa kasar Tanzaniya, domin halartar taron shugabannin kasashen Afirka

 

Shugaba Tinubu

Mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Taron wanda gwamnatin Tanzaniya ta shirya tare da hadin gwiwar bankin raya Afirka da bankin duniya, zai mayar da hankali kan shirin samar da wutar lantarki ga mutane miliyan 300 a Afirka nan da shekarar 2030.

A yayin taron shugabannin kasashen Afirka da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin farar hula, za su tsara dabarun kara samar da makamashi a Nahiyar Afirka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp