Shugaban karamar hukuma a Kaduna ya ƙara wa Limamai alawus


Shugaban karamar hukumar Soba a jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu, ya bayar da umurnin kara kudin alawus da ake bai wa limaman masallacin juma'a da ke yankin.

Da yake jawabi ga limaman, Honarabul Lawal ya bayyana cewa bayan rantsar da shi ya lura da cewa abin da ake bai wa malamai ba yawa kuma ana shafe tsawon lokaci ba a biya su alawus ba.

Shugaban karamar hukumar ya ce wannan ne yasa ya bayar da umurnin sanya karin wasu limamai cikin tsarin biyan alawus din tare da kara yawan kuɗaɗen da ake biyansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp