![]() |
Dikko Umar Radda/Abdullahi Umar Ganduje |
Wadanda suka sauya shekar yawancin sun fito ne daga jam’iyyar PDP, NNPP, Accord Party, da Jam’iyyar PRP.
Guda daga cikin wadanda suka sauya shekar shi ne dan takarar mataimakin gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar PDP a zaben 2015 Rabiu Bakori.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje tare da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa ne suka karbi wadanda suka sauya sheka a yayin kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomin jam’iyyar APC da aka gudanar a karamar hukumar Ingawa a ranar Lahadi.
Ganduje, ya bayyana ranar a matsayin rana mai girma da tarihi a jihar Katsina, ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi wa wadanda suka sauya sheka adalci.
Ya ce jam’iyyar APC ita ce kadai jam’iyyar da ta cancanci shiga da ke yin abin da ya dace ta hanyar isar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan kasa.