![]() |
Shugaba Tinubu |
Zuwan shugaba Tinubu zuwa Dubai na zuwa ne bisa gayyatar shugaban kasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
Mataimaki na musamman ga shugaban Tinubu kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ya sanar da hakan Tinubu a shafin sa na X.
Shugaba Bola Tinubu ya gana da karamin ministan harkokin wajen kasar, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, a lokacin da ya sauka a birnin Abu Dhabi a ranar 12 ga watan Junairu, 2025. A Abu Dhabi.
Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabin da zai bayyana sauye sauyen da gwamnatinsa ta kawo ga Nijeriya, musamman inganta harkokin sufuri, lafiyar al'umma, da ci gaban tattalin arziki.
A yayin ziyarar, Tinubu da tawagarsa za su tattauna da shugabannin kasar don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma lalubo damammaki na huldar tattalin arziki da diflomasiyya.