Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abba Abubakar Aliyu a matsayin babban Manajan Darakta na Hukumar bunkasa wutar lantarki a yankunan karkara (REA).
Wata sanarwa da Bayo Onanuga mai taimaka wa shugaban kan yada labarai ya fitar, ta ce nadin ya fara aiki daga 23 ga watan Junairu 2025.
Abba Abubakar Aliyu ya rike da mukamin mukaddashin manajan daraktan hukumar tun watan Maris na 2024 har zuwa lokacin da aka nada shi.
A baya, ya rike mukamin shugaban sashin kula da ayyuka na shirin samar da wutar lantarki ta Najeriya
Shugaba Tinubu ya yi ammanar cewa, Abba Aliyu zai yi amfani da dimbin ƙwarewar da yake da ita don kara kawo cigaba a hukumar.