Shugaban Amurka Joe Biden zai karrama Messi da jarumin Denzel Washington tare da wasu 17 da lambar girmamawa ta kasar


Shugaba Joe Biden na Amurka zai bayar da lambar girmamawa ta kasar ga wasu sanannun mutane da suka hada da 'yan wasa, da 'yan kwallo da 'yan siyasa da kuma jami'an diflomasiyya.

Daga cikin wadanda tsohon shugaban mai barin gado zai karrama har mawaki kuma ɗan gwagwarmaya Bono, da shahararren dan wasan ƙwallon kwando Earvin Johnson, da zakaran kwallon kafa Lionel Messi, da jaruman Hollywood irin su Denzel Washington da Michael J. Fox, da sauransu.

Sanarwar da fadar White House ta fitar, ta ce wadanda za a karrama jagorori ne na gari da suka bayar da gudummawa wajen ci gaban duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp