Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu zai bar birnin tarayya Abuja a ranar Assabar 11 ga watan Janairu, domin halartar taron tattaunawa kan matsalolin da ke addabar duniya na shekara ta 2025 da zai gudana a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga, ya fitar a yau jumu'a.
A cewar sanarwar, Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, shine ya gayyaci Shugaba Tinubu domin ya halarci taron da zai gudana daga ranar 12 zuwa 18.
Category
Labarai