Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yabawa gwamnonin jihohin kasar bayan da suka amince da kudirin garambawul na dokar haraji, dake gaban Majalisu.
Shugaban ya kuma ya yabawa shugaban kungiyar gwamnonin gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq bisa hade kan gwamnonin da yayi suka aminta da lamarin na haraji.
Ta cikin sanarwar da jami'in yada labaran sa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce gyara fare da yin kwaskwarima ga tsohon tsarin karbar haraji na da matukar muhimmanci.
A karshe ya bukaci Majalisar dokoki da su yi hanzarin sahale kudirin domin ya zama doka da al'ummar Najeriya za su amfana da shi.