Shugaba Tinubu ya umurci jami'an soji da su ci gaba da neman 'yan bindiga da 'yan ta'adda domin ci gaba da kakkabesu

 

Shugaba Tinubu

A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar  Shugaba Tinubu ya jajanta wa sojin kasar sakamakon rashin wasu jajirtattun sojoji guda shida a wani harin ta'addanci da aka kai a ranar 4 ga watan Janairu a wani sansanin sojoji na Sabon Gida a Damboa dake jihar Borno. 


Shugaba Tinubu ya yi kira da ayi cikakken bincike don gano abubuwan da suka haifar da faruwar lamarin don kaucewa  faruwar makamancin harin a gaba.


Sanarwar ta ce Shugaban ya yabawa rundunar sojin bisa martanin da suka mayar musamman bangaren jiragen sama wajen kaddamar da harin da ya yi sanadin halaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata dukiyoyinsu lokacin da sukai yunkurin guduwa.


Sai dai shugaba Tinubu ya bukaci sojoji da kada harin da aka kai musu ya sanyaya musu gwiwa,inda ya umarce su da su ci gaba da farautar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda musamman yankin Arewa maso Yamma, har zuwa sansanonin su domin ci gaba da kakkabesu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp