Shugaba Tinubu ya amince da haramta luwadi a rundunar sojin Nijeriya

Shugaba Tinubu

An haramta wa jami’an sojin Nijeriya yin luwadi, madigo, sanya kayayyakin da basu dace ba, da sauran abubuwan  da ake ganin sun saba wa ka’idojin rundunar.

Haka zalika an hana jami'an huda jiki da nufin  saka Sarka ko Dan kunne ko kuma zanen hotuna a jikin fata wato  (Tatoo )a jiki, da shan  Barasa a yayin da suke aiki ko basa aiki.

Wannan umurnin yana kunshe ne acikin sashe na 26 na kundun rundunar da aka yi wa kwaskwarima da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 16 ga Disamba, 2024.

A wata takarda da jaridar Punch ta samu a ranar Asabar wani bangaren ta yana cewa, “Bai kamata jami’in soji su dinga aikata  luwadi, madigo, da sauran munanan ayyuka ba.

 Haka zalika ba a amince wani jami'in rundunar soji ya dunga irin wayannan ayyuka ba ciki harda yin "Tattoo" dama shan abubuwan da zasu kautarwa mutum hankali a loka2cin yana kan aiki ko baya aiki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp