Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ASUU, ta ce bai kamata bashin da ake bawa dalibai na Karatu NELFUND, ya maye gurbin aiyyukan asusun tallafawa manyan makarantu TETFUND ba.
Kungiyar ta ce zata yi duk mai yiwuwa don ganin cewar ba a kassara ko dakile aiyyukan TETfund ba duba da gagarumin aikin da take na bunkasa fannin Ilimi a Najeriya, tun bayan kafa ta a shekarar 2011.
ASUU tace tsarin bashin kudin karatu wasu 'yan tsirarin dalibai kawai zai amfana sabanin wanda yake taimakawa dukkanin makarantun gaba da Sakandire na Najeriya a karkashin TETfund.
Da yake karin haske kan matsayar ta ASUU, shugaban kungiyar shiyyar Nsukka dake jihar Enugu Raphael Amokaha, yace fito da wasu tsare -tsare dangane da tallafawa Ilimi dai dai yake da kassara aiyyukan TETfund, don haka ba zasu lamunta ba.