Daga A'isha Usman Gebi:
Farashin shinkafa ya fi sauki a kasuwar Mai'adua da ke jihar Katsina arewacin Nijeriya da ake sayar da buhun N145,000, sai dai kuma farashin bai sauya ba dana makon jiya.
Ita kuwa kasuwar Mile 12 International Legas karin N10,000 aka samu a sati nan, a satin daya wuce N150,000 aka sayar da buhun shinkafar hausa a kasuwar, amma a makon nan N160,000 ne kudinta.
Sai kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sai da buhun N160,000 a wannan mako.
A kasuwar Saminaka ta jihar Kaduna N50,000-52,000 ake sai da buhun shanshara na shinkafar a wannan mako, a makon daya gabata kuma aka sai da N55,000.
A bangaren Shinkafar Bature kuwa, farashinta bai canza zani ba daga na makon jiya wanda aka sai da a N95000 a kasuwar Mile 12 International ta jihar Legas a kudancin Nijeriya.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna N98,000 ake sayar da buhunta a makon nan, a makon jiya aka sai da a N95000, karin dubu uku kenan aka samu.
N85000 aka sai da buhun shinkafar waje a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a satin daya shuɗe, to a satin nan ma haka aka sai da.
Da DCL Hausa ta leka a kasuwanni, mun gano farashin masara yafi sauki a kasuwar Saminaka ta jihar Kaduna, wanda ake sayar buhunta N48,000 - 52,000 a wannan mako, a makon jiya kuwa N50,000-55,000 aka sai da ta.
A kasuwar Giwa jihar kuma N58,000 ne kudinta a satin nan.
An samu ragin N1000 guda akan farashin makon jiya, wanda aka sai da N65000 a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, a makon nan ake saidawa N64000 a kasuwar.
Masarar na ci gaba da sauka a kasuwar Mile 12 International Legas da ake sai da buhun a N80,000 cif a satin nan, a satin daya wuce aka sai da N85000.
Farashin wake kuwa yafi rahusa a kasuwar Giwa jihar Kaduna, da ake sai da buhun N107,000
Sai kuma kasuwar Saminaka jihar Kaduna da ake sai da buhunsa N110,000 a satin nan, haka farashin ya ke a makon da ya gabata.
N118,000 aka sai da buhun kananan wake a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a makon daya gabata, sai makon nan ake saidawa N115,000.
Karin N5000 aka samu a wannan mako kan farashin wake a kasuwar Mile 12 International Legas, a makon jiya N150,000 aka sai da buhunsa, a makon nan kuwa ake saidawa N155,000.
Kwalin taliyar Spaghetti yafi tsada a kasuwar Mile 12 International Legas, wanda ake saidawa N21,000 a makon da muke bankwana shi, bayanda a makon jiya aka sai da a N20,500.
Sai kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayar da kwalin taliyar Spaghetti a N18,000 a wannan mako.
Farashin dai na nan kamar na makon da ya gabata a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, wanda aka sayar da kwalinta N17500.
Hukumar kididdaga ta Nijieriya NBS ta ce hauhawar farashin kayan masarufi da aka samu a watan Disamban 2024 da ya kai kaso 34.80, ya faru ne saboda yawan bukatar kayan a lokacin bukukuwan sabuwar shekarar 2025.