SERAP ta yi karar hukumar sadarwa ta Nijeriya NCC kan karin kashi 50 na kudin kira da na data

 

Shugaba Tinubu/SERAP📷

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta shigar da karar gwamnatin shugaba Tinubu kan abinda ta ce rashin adalci da sabawa doka kan karin kaso 50 na kudin sadarwar da hukumar sadarwa ta kasar NCC ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi.

A baya bayan nan ne dai hukumar NCC ta amince da karin kashi 50 cikin 100 na kudaden sadarwa na kira da na data a fadin kasar.

Wanda akai kiyasin farashin kira zai tashi zuwa nai 16.5 a duk minti guda, farashin data 1GB bayanai na nuni da cewa zai tashi zuwa naira 431.25 haka zalika farashin tura sako zai koma naira 6 daga naira 4.

A karar da ta shigar a ranar Juma’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman kotun da ta yi duba kan hukuncin da hukumar NCC ta yanke na baiwa kamfanonin sadarwa a Nijeriya damar karin kaso 50 cikin dari na sadarwa,abinda ta kira rashin adalci tare da take hakki ga 'yan kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp