![]() |
Gwamnan Kaduna Malam Uba Sani |
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da shugaba Bola Tinubu ke yi zai sake farfado da Nijeriya idan aka yi hakuri.
Gwamnan ya bayyana hakanne a yayin wata lakca da wata kungiya ta shirya inda ya kara da cewa shugaban ya kuduri aniyar dora kasar kan turba da ci gaba mai dorewa.
Gwamnan ya ce akwai bukatar al'ummar Nijeriya su kara hakuri da juriya, ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba 'yan kasar za su fara jin daɗin tasirin sauye-sauyen.