Sabuwar Shekara: Tinubu ya yi alkawarin bunkasa samar da abinci da rage hauhawar farashi zuwa kashi 15 a 2025


Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar wa 'yan kasar kudirin gwamnatinsa na bunƙasa samar da abinci da kuma rage hauhawar farashi zuwa kashi 15 ta hanyar bunkasa tattalin arziki a sabuwar shekarar 2025

A cikin sakon barka da sabuwar shekara da ya aike wa 'yan Nijeriya, Shugaba Tinubu ya bayyana saukar farashin fetur da ƙaruwar kudaden ajiya na kasa da kuma farfaɗowar darajar naira, a matsayin wasu alamomin da ke nuna cewa tattalin arzikin kasar na kan hanyar ci gaba.

Shugaban ya kara da cewa kasuwar hannun jari ta kasar na kara bunkasa tare da samar da kudaden shiga haka kuma masu zuba hannun jari daga kasashen waje na ci gaba da ƙaruwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp