"Saboda yawan yin maganganuna ne yasa aka kai ni gidan kaso" - Tsohon shugaban Nijeriya Obasanjo


Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda aka kai shi gidan yari a lokacin mulkin Janar Sani Abacha shekara ta 1995, saboda yadda yake sharhi akan abubuwan da su ka shafi Nijeriya da kasashen waje.

Obasanjo ya kara da cewa kudirin ceto Nijeriya daga rugujewa ne ya sa ya tsaya takarar shugaban kasa a 1999.

Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da matasa shugabannin gobe 15 wanda dakin karatunsa ke shiryawa a birnin Abeokuta, jihar Ogun.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp