Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce ta kama mutane 575 da ake zargi da aikata laifuka daban daban a shekarar 2024

 

'Yan sanda

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmad Musa, wanda ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce an samo bindigogi kirar AK-47 guda 9 da harsashi guda 341 sai kuma wasu kirar gida guda 4 da alburusai masu tarin yawa.

Sauran da aka samu baya ga makaman sun hada da motoci uku, barayin shanu 97, tumaki 29 da jaki daya yayin da aka ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su a cikin wannan lokaci.

Sai dai ya ce nasarar an sameta ne bisa jajircewar jami'an 'yan sanda da kuma dabarun aiki da suke da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp