Rundunar sojin saman Nijeriya ta karbi wasu jiragen yaki 12 domin ci gaba da luguden wuta ga 'yan ta'adda

 


Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta karbi wasu jiragen yaki 12 da za su taimaka mata wajen yaki da matsalar tsaro.

Babban hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar, ne ya sanar da hakan a Abuja lokacin ganawa da tsoffin sojoji a jihar Kaduna.

Hassan Abubakar ya ce rundunar ta dukufa wajen yaki da matsalar 'yan ta'adda kuma zuwa kowane lokaci za su sake karbar wasu jiragen 10 daga kasar Italy.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp