CDS Christopher Musa |
Kwamandan rundunar hadin gwiwa da ke kula da yankin Arewa maso yamma, Operation Fansan Yamma’ Maj, Gen. Oluyinka Soleye ya bayar da wannan umurni ne a ranar Juma’a a lokacin da ya kai ziyara ga sojojin da ke Balle, karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato.
Da yake jawabi ga sojojin, Soleye ya yi kira da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, tare da ba su tabbacin samun cikakken goyon bayan hedkwatar rundunar.
Ya kuma umurce su da su yi duk abin da za su iya don kawar da kungiyar ta Lakurawa ko kuma su tabbatar da koras su gaba daya daga yankin.
Sai dai Soleye ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu, inda ya yi alkawarin bayar da goyon baya ga rundunar ta yadda za a samu nasarar aikin.