Rundunar sojin saman Nijeriya ta nuna damuwa akan rahotannin da ke nuna cewa farmakin da sojoji suka kai a maboyarsu Bello Turji a jihar Zamfara, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula.
Mai magana da yawun rundunar, Akinboyewa ya ce sun yi iya kokarinsu wajen kauce wa irin wannan matsala.
Rahotanni sun bayyana cewa da marecen Asabar ɗin makon da ya gabata, jirgin saman sojojin Nijeriya ya yi luguden wuta kan wasu Askarawan jihar Zamfara a kauyen Tungar Kara na karamar hukumar Maradun, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 16.
Category
Labarai