Wasu mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP mai adawa a Nijeriya sun nuna amincewar su da hukuncin kotu na baya bayan nan da ya soke zaben shugabannin jam'iyyar a jihar Rivers.
Shugabannin sun bayyana hakan ne a lokacin da suka ziyarci Gwamna Siminalayi Fubara a fadar gwamnatin jihar dake Fatakwal.
Tawagar shugabannin karkashin jagorancin Sakataren yaɗa labarai na PDP na kasa Debo Ologunagba, sun ce Fubara shine jagoran jam'iyyar a Rivers
Category
Labarai