RIkicin jam'iyyar PDP mai adawa a Nijeriya kan mukamin sakataren jam'iyya ya dauki wani sabon salo, bayan da wasu mambobin jam'iyyar suka yi zanga zanga kan karbe hedikwatar jam'iyyar.
Jam'iyyar wadda ke hutu ta tsara dawowa aiki ne a yau Litinin, sai dai magoya bayan Sanata Sam Anyanwu dake adawa da mika mukamin sakataren jam'iyya ga Sunday Ude-Okoye sun yi zanga-zanga a harabar jami'iyyar, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Kotun daukaka kara dake Enugu ce dai ta yanke hukuncin cewa Sunday Ude-Okoye shine halastaccen Sakataren Jam'iyyar PDP.
Category
Labarai