Rundunar 'yansandan jihar Jigawa ta ce mutum 9 ne suka rasa rayukansu biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin Fulani da Makiyaya a yankin Gululu, na karamar hukumar Miga.
Tuni da aka dauko gawarwakin mutanen 9 da suka mutu a yayin fadan da ya tsallaka har zuwa yankin karamar hukumar Jahun.
Jami'an tsaro sun ce rikicin ya tashi ne saboda zargin da wasu manoma ke yi cewa makwabtansu makiyaya sun yi musu sata a shago.