![]() |
Malam Dikko Umaru Radda |
Wasu rikakkun 'yan bindiga guda biyu a jihar Katsina sun mika wuya tare da makamansu da wasu mutane sama da 15 da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Batsari da ke jihar.
'Yan bindigar da suka mika wuyan sun hada da Abu Radde da Umar Black.
An alakanta mika wuyan nasu da zafafan hare-haren da sojojin hadin gwiwa na Operation fansar yamma da sauran jami’an tsaro ke cigaba da gudanarwa a yankin.
Wasu majiyoyi sun shaidawa gidan talabijin na Channels a ranar Litinin cewa bikin mika wuya da aka gudanar a ranar Lahadi ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da wasu wakilai daga sojoji da shugabannin gargajiya da na addini a yankin.