![]() |
Bill and Melinda |
Da yake bayani a wata hira da jaridar Times a London, dan kasuwan dan kasar Amurka mai shekaru 69 ya bayyana cewa akwai kura kurai da ya yi a rayuwarsa amma kuskure mafi girma shine rabuwa da matarsa Melinda da suka yi shekaru kusan 27 suna tare
Attajirin Bill da tsohuwar matarsa Melinda sun yi aure a shekarar 1994 kuma suna da yara uku - Jennifer mai shekaru 28,da Rory mai shekaru 25,sai Phoebe mai 22.
Ma'auratan, sun ba da sanarwar rabuwar su a hukumance a watan Mayu na shekarar 2021, wanda a baya aka yi ta zargin sun rabu dama kafin sanarda rabuwar ta su a hukumance.