Gwamnatin Nijeriya za ta karbi bakuncin taron samar da rigakafin cutar Lassa Fever na kasashen yammacin Afrika da zai gudana a ranar Laraba 15 ga watan Janairu.
Ministan Lafiya Farfesa Muhammad Pate ne ya bayyana hakan a firarsa da gidan talabijin na Channels.
Cutar zazzabin Lassa dai annoba ce da ta hallaka mutane 191 kuma take yin barazana ga jihohin Nijeriya dama wasu kasashen Afrika.
Category
Labarai