Nijeriya ta shirya karbar 'yan kasar da Shugaban Amurka Donald Trump zai kora - Hukumar NiDCOM


Hukumar lura da 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM, ta ce ta shirya don karbar 'yan kasar mazauna Amurka da Shugaba Trump zai kora.

Yayin wata tattaunawa da Jaridar Vanguard, daraktan yada labarai na hukumar ta NIDCOM Abdur-Rahman Balogun a ranar Talata, ya ce ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ta kammala shirin karbarsu.

Balogun ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta kafa kwamitoci daga ma'aikatun gwamnati daban- daban da zasu lura da dawowar 'yan Najeriya daga Amurka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp