Bankin ci gaban ƙasar China ya sanar da bai wa Nijeriya bashin dala miliyan $254.76m domin kammala aikin layin dogo da ya tashi daga Kano zuwa Kaduna.
A cewar wani bayani da bankin ya fitar a ranar Talata, kudaden wata alama ce ta irin kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin Nijeriya da China.
A shekarar da ta gabata ne Shugaba Tinubu ya bayar da tabbacin zai kammala aikin layin dogon Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano kuma gwamnati na sa ran kammala na Kaduna zuwa Kano a karshen shekarar 2025.
Category
Labarai