Gwamnatin Nijeriya ta ce ta karbi miliyan 52.88 daga kasar Amurka da aka kwato wadanda aka alakanta da tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Madueke.
Babban lauya na kasa kuma ministan shar'ia Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sanya hannu kan yarjejeniyar mika kadarorin tsakanin Nijeriya da Amurka a Abuja.
Fagbemi ya ce dala miliyan hamsin daga cikin kudaden za a yi amfani da su a karkashin shirin bankin duniya na samar da lantarki a yankunan karkara, yayinda sauran dala miliyan biya za a sanya su a inganta bangaren shari'a domin ya ki da cin hanci da rashawa.
Category
Labarai