Gwamnatin Nijeriya ta ce dole ne a kara kudin amfani da layin sadarwa na kasar domin bunkasa bangaren da kuma hannayen jari da aka zuba.
Sai dai gwamnatin ta ce karin da za a yi ba zai kai kashi 100 ba kamar yadda kamfunna ke bukata.
Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani Dr Bosun Tijani ne, ya bayyana hakan a Abuja, jim kadan bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki kan harkokin sadarwa.
Category
Labarai