Najeriya ta karbi bashin sama da biliyan 1 daga bankin bunkasa kasashen Afirka AfDB

Najeriya ta samu sahalewar karbar bashin dala biliyan 1.1 daga bankin bunkasa kasashen Afirka AfDB don samar da wutar lantarki ga al'ummar kasar miliyan 5 zuwa karshen shekarar 2026.

Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana haka ta bakin ministan samar da lantarki Adebayo Adelabu ya yi a taron kwana biyu na harkokin lantarki a Afirka  da aka gudanar a birnin Dar es Salam na kasar Tanzania, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana.

Shugaban ya gode wa shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwunmi Adesina da na bankin duniya Ajay Banga, bisa wadannan kudaden da suka bai wa Nijeriya domin bunkasa samar da lantarki ga al'ummar kasar.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp