Na ki amincewa da yin tsafi domin zama gwamna - Gwamnan Bayelsa


Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, ya bayyana yadda ya kaucewa shiga tsafi kuma sai imanin da yake da shi ya sa ya ci zaben gwamnan jihar da aka gudanar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamanan Daniel Alabrah, ya fitar a wannan Asabar, wadda ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin wani buki da aka shirya.

Gwamna Diri ya ce a shekara ta 2020, wani babban muutun ya gayyace shi a Abuja kuma ya shawarce shi da ya yi tsafi idan har yana son ya zama gwamna, amma sai ya yi watsi da shawarar.
 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp