Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana dalilinsa na janye adawar da yake yi da dokar haraji, yana mai cewa an magance korafin da yake da shi.
Gwamna Sule, wanda ke cikin jagororin yankin arewacin Nijeriya da su ka yi fatali da dokar, ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels.
Ya ce tun da farko shi ba adawa yake da dokar gaba ɗaya ba amma abinda ke cikin dokar, kuma a cewarsa suna yin wannan ne don bai wa kowa damar fadin albarkacin bakinsa kafin aiwatar da dokar.