Akalla mutane 7 ne ake hasashen sun mutu yayinda wasu 80 suka ji munanan raunuka sanadiyar motar dakon mai ta fashe a kan hanyar Maje-Dikko dake karamar hukumar Suleja ta jihar Niger.
Shaidun gani da ido sun shaida wa jaridar Dailynigerian cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar lokacin da ake juye mai daga motar zuwa wata.
Jami'an tsaro da na kashe gobara sun hallara a wurin domin kashe gobarar da ta tashi.
Category
Labarai