Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya ta ce mutum 573,519 ne su ka cike shafin neman aiki da ta buɗe a kasa da mako guda, domin neman gurbin ma'aikata 3,927.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Maiwada, ya ce tuni da aka rufe shafin saboda lokacin da aka ɗiba ya cika.
Ya ce bangaren da za a dauki ma'aikatan yana da yawa aikin na tafiya yadda ya kamata.
Category
Labarai