Mutanen daji sun shigo sun yi garkuwa da wasu iyalai a Abuja babban birnin Nijeriya


Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Chikakore da ke Kubwa a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya, inda suka yi garkuwa da wani mutum da matarsa da dansa tare da wasu mutane biyu.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa masu garkuwa da mutanen sun kai kimanin mutun 30 kuma dukkanin su dauke da bindigogi kirar AK-47, inda suka nufi gidan wani mai suna Adefija Micheal Akinropo, wanda aka yi garkuwa da shi tare da iyalansa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp