Mutane 86 suka mutu sanadiyar fashewar motar man fetur jihar Neja, an binne 80 a kabari daya - Hukumar NSEMA

Biyo bayan fashewar motar man fetur a mararrabar Dikko Junction, dake karamar hukumar Gurara jihar Niger, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar NSEMA ta ce zuwa yanzu mutum 86 suka mutu.

Wani bayani da daraktan yada labarai na hukumar Abdullahi Baba-Arah ya fitar, ya ce hukumar ta tattara gawarwakin mutanen ne tare da taimakon jami'an karamar hukumar Gurara da kuma jami'an sa kai.

Daga cikin wadanda suka mutu an binne mutum 80 a kabari daya a cibiyar kafiya ta Dikko yayinda biyar aka hannunta su ga 'yan uwansu, mutum daya kuma ya mutu daga baya saboda raunin da ya ji.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp