Mutane 200 ne suka yi rajistar zuwa aikin hajjin bana da hukumar jin dadin alhazai ta jihar Taraba

 


Jami’in hulda da jama’a na hukumar Hamza Baba Muri ne ya bayyana hakan a wata zantawa da Daily Trust ranar Litinin.

Muri ya ce duk da cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware kujeru 1,400, na adadin maniyyatan da za ayi wa rijista kawo yanzu a Taraba shine mafi karancin shekaru a ayyukan Hajji a jihar.

A cewarsa, a shekarar da ta gabata, mahajjata 1007 ne suka sauke farali daga jihar Taraba. Sakamakon yawan maniyyatan da suka yi rijista, yanzu haka hukumar ta fara rangadi a fadin jihar domin jawo hankalin mutane da za su biya kudin aikin hajjin.

Ya kara da cewa za a ziyarci dukkan kananan hukumomin jihar kuma suna fatan adadin maniyyatan jihar na bana zai karu fiye da na baya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp