Muna sane da korafe-korafen al'umma kan tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatinmu, zamu duba mu yi gyara inda ya dace - Kashim Shettima


Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa gwamnatin su zata ci gaba da samar da romon mulkin dimokuradiyya ta hanyar gyara tattalin arziki tare da tabbatar da tsaro ga al’umma, yaki da cin hanci da rashawa.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taro wanda akai ma laƙabi da Karfafa dimokuradiyyar Najeriya, tare da hanyoyin gudanar da shugabanci nagari.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp