![]() |
Ministan kwadago Muhammad Dingyadi |
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammad Dingyadi, ya ce ma’aikatar na bukatar karin kudade cikin kasafin kudin 2025, domin bunkasa ayyukan ta.
Ya ce za a yi amfani da kudaden musamman wajen gyarawa, sake ginawa da kuma samar da kayan aiki ga cibiyoyin bunkasa sana’o’i da ke karkashin ma’aikatar da hukumomi a fadin kasar, da nufin samar da ayyukan yi ga al'umma.
Dingyadi ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kudin 2025, a gaban kwamitin majalisun dokoki da na dattawa. Ya ce jimillar kasafin naira biliyan 46 da aka ware wa ma’aikatar a wannan shekarar ba zai wadatar ba wajen cimma manufofin da ake so a cimma.
Dangyadi ya jaddada cewa samar da ayyukan yi ta hanyar bunkasa fasahar zamani na da matukar muhimmanci wajen cimma wani bangare na manufofin gwamnatin shugaba Tinubu.