Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, ya ce ba zai bari giyar mulki ta sauya shi ba daga yadda yake.
Gwamnan ya bai wa al'umma tabbacin zai tsaya kan alkawuran da ya yi wa al'ummar Rivers domin kawo ci gaba a jihar.
Gwamna Fubara ya yi wadan nan kalaman ne lokacin da dattawa da masu ruwa da tsaki na jihar suka kai masa ziyara domin taya shi murnar cika shekar 50 da haihuwa.
Category
Labarai