Hukumar kula da babban birnin tarayya ta cika makil da masu harkar gidaje da kuma 'yan siyasa masu filaye a Abuja, bayan da Ministan birnin Nyesom Wike, ya kwace wasu filayen sanannun mutane 568 a yankin Maitama II a Abuja.
Wani mai harkar gidaje a Abuja Ameh Daniel ya shaida wa jaridar Punch cewa masu filayen na rige-rigen zuwa ne domin biyan kudin takardun filayen domin tsira da kadarar da suka mallaka.
Sai dai wani dan majalisar wakilai Mista Oluwole Oke ya bukaci WIke da ya kara wa'adin biyan kudin takardun ga mutane 568 da aka kwace wa filaye.
Category
Labarai