![]() |
Vitor Reis |
Manchester City ta sanar da kammala daukan matashin dan wasan baya Vitor Reis daga kungiyar Palmeiras ta Brazil kan kudi Euro miliyan 29.6.
Dan wasan dan kasar Brazil mai shekaru 19, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da rabi da kungiyar da ke buga gasar gasar Firimiyar ta kasar Ingila.
Reis ya bayyana farin cikinsa na zama daya daga cikin 'yan wasan Manchester City, da ke cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya.